Wahalar Da Ake Sha A Gwamnatin Tinubu, Pro-max Ce Akan Ta Buhari – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce idan har zuwa yanzu gwamnatin APC karkashin jagorancin Bola Tinubu ba ta gane irin wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki ba, hakan na nufin tun farko ba ta shirya gudanar da mulki ba.

Atiku, wanda ya yi magana ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya bayyana cewa abin takaici ne yadda gwamnatin Tinubu ta bari har sai da yan Najeriya su ka fito kan tituna domin jawo hankalinta kan mawuyacin hali da aka tilasta musu rayuwa a ciki.

Ya ce, “Tabbas akwai kalubale a baya, shi ya sa aka zaɓe ka. Mun san abubuwa da yawa an yi kuskure a lokacin Buhari.

“Tattalin arzikin kasar ya shiga koma-baya har sau biyu a karkashin gwamnatin APC da ta shude saboda ba ta san komai ba kan tattalin arziki, jajircewa, cin hanci da rashawa ya yi yawa.

“Duk abin da Buhari ya yi ba daidai ba muna ganin na sama da shi a karkashin Tinubu. Abin da muke gani a yau shine Buhari pro-max,” in ji shi.

 

 

    Related Articles

    Ooops! Join The Community To View The Comments

    We would love to hear from you!

    Please record your message.

    Record, Listen, Send

    Allow access to your microphone

    Click "Allow" in the permission dialog. It usually appears under the address bar in the upper left side of the window. We respect your privacy.

    Microphone access error

    It seems your microphone is disabled in the browser settings. Please go to your browser settings and enable access to your microphone.

    Speak now

    00:00

    Canvas not available.

    Reset recording

    Are you sure you want to start a new recording? Your current recording will be deleted.

    Oops, something went wrong

    Error occurred during uploading your audio. Please click the Retry button to try again.

    Thank you

    Send your recording